Shugaba Buhari Ya Jajantawa Turkiyya Da Siriya Kuma Ya Yi Alkawarin Tallafi
Ya kuma jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwa da abokan arziki a girgizar kasar da ta afku a garin Gaziantep da ke kudancin kasar Turkiyya.

Shugaban ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa, ya kuma ba da tabbacin cewa addu’o’i da tunanin ‘yan Nijeriya na tare da dimbin wadanda wannan mummunan bala’i da fargaba ya shafa.

A matsayinsa na aminin Turkiyya da Siriya, Shugaba Buhari ya ce Najeriya a shirye take ta ba da cikakken goyon bayan ta ta kowace hanya.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like