Shugaba Buhari Ya Mika Sakon Ta’aziyya Ga Shugaba Rauhani Na Iran


 

 

4bmt92d0e5247dlcgj_800C450

 

 

 

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar Ayatollah Hashimi Rafsanjani zuwa ga shugaban kasar Iran Hassan Rauhani.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a cikin sakon da shugaba Buhari ya aike wa shugaba Rauhani, ya bayyana cewa hakika an yi babban rashi na mutumin da ke da bababn tasiri ta fuskar siyasa da gagarumin ci gaba da kasar Iran ta samu.

Shugaba Buhari ya ce hakika ayyukan da Rafsanjani ya yi wajen ci gaban kasarsa, za su ci gaba da wanzuwa a kasar Iran, tare da bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi na wani babban jigo a dukkanin bangarori na siyasa da zamantakewa da ci gaban tattalin arziki a kasar ta Iran.

Shugaba Rauhani ya yi godiya ga shugaba Buhari dangane da sakon nasa tare da yin fatan alkhairi ga dukkanin al’ummar Najeriya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like