Shugaba Buhari ya Musanta Jita Jitan Cewa Gwamnatinsa Za ta Yi Bincike akan Sarki Sanusi


 

 

A jiya Litinin, fadar shugaban kasa Buhari ta musanta jita jitan da ke yaduwa a kafafen yada labarai da ke nuna cewa gwamnatin tarayyar za ta shiga binciken akan tsoffin shugannin babban bankin Nijeriya (CBN) Sarkin Kano Sunusi Na II da farfesa Charles Soludo.

Rahotannin da aka wallafa a kafafen sada zumuntan a ranar lahadin da ta gabata sun bayyana cewa gwamnatin tarayyar ta gama shirye shiryen fara bincike akan tsoffin shugabannin biyu a sakamakon ra’ayoyinsu da suke bayyanawa game da halin da tattalin arzikin kasa ya shiga.

Haka kuma rahotan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta sanya sarki Sanusi da Soludo a cikin wadanda gwamnatin ke zargi ga me da wasu cuwa cuwa da suka faru a yayin da suke rike da mukami a babban bankin

A wani sako da ya wallafa a shafin Twitter, babban mai taimakawa shugaban kasa a kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai san da wannan batu ba.

Ya yi tambaya Shin daga ina wannan rahotan ya fito? Ya ce a kundin mulkin kasa wanda shugaban Buhari ya yi rantsuwa zai bi, ba laifi bane wani ya baiwa gwamnati shawara.

 

 

 

cc: Alummata

You may also like