Shugaba Buhari Ya Umarci Hukumar DSS da ta Mika Binciken Alkalai Ga Hukumar EFCC


 

wp-1477380261544.jpg

Rahotanni na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari bai ji dadin yadda hukumar ‘yan sanda ta farin ka ya ke gudanar da bincike akan alkalan Nijeriya ba, bayan da wasu lauyoyi suka yi duba akan hujjojin da hukumar ta ce ta samu a sumamen da ta kaiwa alkalan makonnin da suka gabata.

A don haka ne shugaban kasar ya umarci hukumar da ta mika binciken ga hukumar da ta fi kwarewa a wannan bangare wato EFCC.

A wani rahoto da jaridar Sahara Reporters ta wallafa, ta bayyanan cewa jnkiri da aka samu daga bangaren DSS game da shigar da alkalan kotu, da kuma yadda suka gudanar da inciken da rashin kwarewa shi ya baiwa alkalan damar su fara janye wasu daga cikin maganganun da suka yi, su kuma fara dagula hujjojn da ke akan su.

 

Da ma dai tun a farko, an bukaci hukumar ta DSS da ta hada karfi da karfe da hukumar ta EFCC domin ganin an yi bincike mai kyau, sai dai hukumar ta DSS ta ki gamsuwa da hakan a bisa kishi da ke tsakanin hukumomin biyu, inda ta zabi ta yi aiki da hukumar ‘yan sanda a maimakon ta.

Sai dai al’amarin ya dagule yayin da ka fara zargin cewa su ‘yan sandan da aka hada kai da su na bayarda da bayanan sirri game da binciken ga alkalan. A bangaren jahar Rivers kuma an zargi ‘yan sandan da bayyanawa gwamnan jahar Nyesom Wike shirin hukumar na kawo sumame.

You may also like