Shugaba Buhari Ya Yi Taron Bankwana Da Majalisar MinistocinsaShugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wani taron bankwana na majalisar zartarwar sa da aka yi a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

A taron, shugaban ya yi bankwana da manyan jami’an gwamnatin sa da ma sauran ma’aikatan fadar Aso Rock.

Taron bankwana

Taron bankwana

Taron ya samu halatar dukkan ‘yan majalisa da suka nuna alamun juyayin kammalar mulkin don tunkarar sabuwar rayuwa.

Duk da haka shugaban ya yi jawabi yana mai cewa ta yiwu wasu su ci gaba da zama a gwamnati amma shi da mai kama da shi za su yi nesa da gwamnati.

Taron bankwana

Taron bankwana

Shugaban ya kuma jinjina wa jam’iyyar APC da ya ce ita ta ba su damar kama madafun iko, ya kuma bukaci jam’iyyar ta ci gaba da tallafawa.

Ministan yada labarai Lai Muhammed ya ce an ba dukkan ministoci dama su yi bayani na bankwana, a yayin da suke tattara takardun mika ragama ga gwamnati mai shigowa.

Taron bankwana

Taron bankwana

Shugaba Buhari ya gode wa Allah da ya ba shi damar shugabanci, ko da yake bai ambaci batun talakawa ba, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakinsa Femi Adeshina ta nuna.

‘Yan kasar dai na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu game da gwamnatin Buhari ta tsawon shekaru 8, yayin da wasu suka yaba wasu ko sun kagu su ga bayanta.

A ranar Litinin 29 ga watan Mayu ne dai za a yi bikin rantsar da sabuwar gwamnatin.

Saurari rahoton a sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like