Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Kai Ziyarar Aiki Ta Yini Biyu Jihar Jigawa A Ranar Litinin 7 Ga Watan Mayu Shekarar 2018.
A Yayin Ziyarar Shugaba Buhari Zai Bude Wasu Katafaren Aiyukan Da Gwamnatin Jihar Jigawa Ta yi A Ciki Da Wajen Garin Dutsen Babban Birnin Jihar Jigawa.
Aiyukan Da Shugaban Kasa Zai Bude Sun Hada Da, Sabbin Tituna, Gidajen Ruwan Sha Da Sababbin Asibitin Specialist Da Sabuwar Makarantar Aikin Jinya, Da Sauran Aiyukan Alkairi Da Gwamnatin Jihar Jigawa Ta yi Karkashin Jagorancin Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar.