Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Jihar Taraba Yau


Bisa ga kasha-kashe da ya faru a jihar Taraba karshen makon da ya gabata, ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar ban mamaki jihar Taraba yau.

Jaridar Vanguard ta bada wannan rahoto ne da safiyar yau Litinin, 5 ga watan Maris, 2018. Wannan labari na fitowa ne bayan ana sa ran shugaban kasan zai je kasar Ghana domin halartan taron murnan zagayowar ranan samun yanzin kasar shekari 61.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan ne a shafin sada ra’ayi da zumuntarsa na Facebook da daren jiya Lahadi.

Jama’a na ganin cewa Buhari ya amsa kukan jama’a ne bayan jama’a masoya da yan adawarsa suka caccakesa akan cewa ya halarci auren diyar gwamnan jihar Kano amma yayi kunnen kashi da kiran mutane cewa ya ziyarci iyayen yan matan Dapchi da kisan Mambila.

Wasu sun kara da cewa da alamun ba shugaba Buhari ke mulki ba saboda bai iya zuwa inda ya ga dama lokacin da ya ga dama.

You may also like