SHUGABA BUHARI ZAI NEMI KARIN IKO A NAJERIYA 


Wannan dai na zuwa ne bayan da tattalin arzikin na Najeriya ke kara shiga rudani, a hannu guda kuma al’umma a kasar na jin jiki.
Shugaba Muhammadu BuhariShugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai nemi karin karfin iko daga bangaren majalisa ta yadda zai dauki matakai na gaggawa dan farfado da tattalin arzikin kasar.

Wata majiya ta gwamnatin kasar ta bayyana haka a ranar Litinin din nan. Abin da ke zuwa bayan da tattalin arzikin kasar ke samun koma baya, yayin da a bangare guda take kasa fitar da albarkatun mai yadda ta saba saboda aiyukan masu fasa bututun mai a yankin Niger Delta.Gwamnatin dai za ta gabatar da kudurin mai taken ” Daidaita tattalin arziki cikin gaggawa” wanda za a mika shi ga majalisa nan gaba.

You may also like