Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin karbo rancen dala kusan biliyan 30 daga kasashen waje.
Shugaban ya bayyana bukatar haka ne a wata wasika da ya gabatar wa Majalisar Dokoki ta kasar, wadda shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara suka karanta a zaurukan Majalisun a yau Talata.
A wata wasikar ta biyu kuma, Shugaba Buhari ya bukaci dauke wasu kudi Naira biliyan 180 da doriya daga ayyukan da aka shirya kashe su tun farko a kasafin kudi na 2016 zuwa samar da wasu muhimman bukatu a jihohin kasar 36 da yankin Babban Birnin Tarayya.
Nijeriya dai na cikin kungiyar kasashen da ke da albarkatun man fetur, OPEC, amma a karo na farko cikin kusan shekaru 20, tattalin arzikin kasar ya shiga halin ha’ula’i, bayan faduwar da farashin man fetur ya yi a kasuwannin duniya.
Rancen na kasashen waje dai ya kunshi rancen dala biliyan goma sha daya da kusan miliyan dari biyu na gudanar da wasu ayyuka, da rancen gudanar da ayyukan samar da ababen more rayuwa na musamman wanda ya kai dala biliyan goma da kusan miliyan dari shida, da takardun lamuni na Turai wadanda darajarsu takai dala biliyan hudu da rabi, da kuma tallafi ga kasasfin kudi na gwamnatin tarayya wanda ya kai dala biliyan uku da rabi.
Cinikin danyen man fetur ne ke samar da kashi biyu bisa uku na kudin da gwamnatin Nijeriyar ke samu, lamarin da ya sa kasar ta fada matsalar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya.