Shugaba Muhammadu Buhari da yardar Allah zai kai ziyarar aiki jahar kaduna inda zai bude wani katafaren wurin sauke kayan jirgin kago Wanda akafi Sani da Inland Dry Port a turance a unguwar kakuri dake garin kadunar
Shidai wannan wurin wanda shine irinsa na farko a Najeriya anasa ran zai dinga karbar kayan jirgin kagon ne daga jahar Lagos ta hanyar jirgin kasa ko kuma ta hanyar mota
Wannan zai baiwa masu shige da ficen kaya a ciki da wajen arewacin Najeriyar damar shigowa ko fitar da kayan ta jahar kaduna
Kuma shi wannan wurin anasa ran zai samarda ayyukanyi akalla 5000 ga Jama’a