Shugaba Yoon Suk na Koriya ta Kudu na ziyara a a Burtaniya – DW – 11/20/2023



A Litinin din nan shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol ke fara wata ziyarar aiki ta kwanaki 4 a Burtaniya, da nufin karfafa alaka ta tsaro da tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu, don samun damar tunkarar barazanar tsaron da makwabciyarta Koriya ta Arewa ke mata, da ma sauran makotanta.

A wata ganawa da jaridar The Telegraph, Mr Yoon ya ce dalilai da dama ne suka sanya shi kai ziyarar don neman tallafi, wadanda suka hada da batun yakin Gaza da na Ukraine, da kuma yadda alaka tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa ke kara yaukaka, har ma da batun barazanar makwabciyarta China.

Mr Yoon zai ziyarci fadar Buckingham don ganawa da Sarki Charles na Burtaniya, sannan kuma ya tattauna da firaminista Rishi Sunak daga bisani.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like