Shugaban Amurka Barack Obama da mataimakinsa Joe Biden da tsohon shugaban kasar George W. Bush sun hallara a birnin Dallas dake jihar Texas saboda yiwa ‘yansandan birnin ta’aziyar mutuwar biyar daga cikinsu sanadiyar harbesu da aka yi.
Shugaba Obama da mataimakin shugaba Joe Biden da kuma tsohon shugaba George W. Bush zasu hallara a wannan birni inda wani dan harbin kwanton bauna ya bindige ‘yan sanda 5 har lahira, ya kuma raunata wasu 4 tare da farar hula 2 lokacin wata zanga zangar lumana a makon jiya.
Wani babban fada a Dallas, Rev. Frederick Haynes, ya fadawa shugaba Obama cewa yana goyon bayansa sosai, amma kuma yana son yayi tattaki har zuwa Minnesota, watau daya daga cikin wuraren da ‘yan sanda suka kashe bakaken fata na baya bayan nan.
Gobe laraba, gwamnati zata hada jami’an ‘yan sanda, da ‘yan raji da masana da kuma masu rajin kare hakkin mutane a fadar White House domin Tattauna hanyar da za a iya samo mafita daga wannan lamarin.