Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya bada umurnin ga jihohin kasar su biyar albashin ma’aikata daga kudaden basussuka da aka mayar masu
Jaridar Daily Trusta ta Nigeria ta nakalto mai bawa shugaban kasa shawara kan al-amuran watsa labarai Garba shehu yana fadar haka a jiya Alhamis. Shehu ya kara da cewa shugaban ya umurci gwamnonin jihohi da suka kashe akalla kashi 25% na rarar kudaden bashin da aka mayar masu wajen biyan albashin maikatansu da kuma wadanda suke karban Fansho.
Shehu ya kara da cewa shugaban ya da umurnin sakin kudade Naira billion 552.74 ga jihohi 33, cikin kaso kaso 4 ga dukkan jihohin da ma’aikatansu suke binsu bashi na albashi, ya kuma kara da cewa jihohin zasu karbi kaso na farko, wato 1/4 kudaden kafin karshen wannan makon.
Shehu ya ce shugaban ya bukaci ministan kudin kasar Kemi Adeosun da ya tabbatar da cewa rashin biyan albashin ma’aikata da kuma kudaden fensho na wadanda suka yi ritaya kada bai sake zama matsala ba a kasar.