A jawabin da yayi a shafin nasa na Facebook, Mark Zuckerberg ya shaidawa duniya cewa, a yanzu haka sun kara yaren Hausa daga cikin yarurruka guda 100 da ake amfani da su a shafin facebook din.
Ya kara da cewa, babban dalilin kara yaren shine saboda yawan mutanen da suke mu’amala da kuma sada zumunci da harshen hausan maimakon harshen Turanci. Ya bayyana adadin mutane sama da billiyan daya (1 billion) da cew sune suke amfani da Shafin na Facebook da harshen a saboda haka ne ya dauki alkawarin sanya Harshen na Hausa a cikin jerin yarurrukan Facebook.
Masana harshe dai sun bayyana cewa wannan ba karamin ci gaba bane ga Harshen na hausa inda yanzu duniya zata kara sanin muhimmancin yaren a duniya da kuma kara baiwa Masu amfani da yaren daraja a idon Duniya.
Mark Zuckerberg, tun ranar farko daya ziyarar ci Nijeriya, ya bayyana kudurin sa na saka Harshen Hausa a shafin nasa na Facebook inda ya cika wannan alkawari a jiya 1 ga wata oktoba, 2016.
Bayan hausa, yaren Fulatanci ma ya samu shiga shafin na Facebook wanda yace fulani ma baza a barsu a baya ba.
Kudirin nasa dai ya samu suka daga wasu daga cikin ‘yan kudancin Kasar nan masu Yaren Yarabanci da kuma yammaci masu yaren inyamuranci, inda suke ganin cewa suma yarukansu sun cancanta da shiga shafin na Facebook. Wanda muke ganin kawai suna nuna Kishin sune karara na rashin jin dadin Daukakar da Allah yayiwa yaren na Hausa da kuma Fulatanci.