Shugaban Facebook ya ziyarci Najeriya.


 

 

Shugaban shafin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg, ya ce yana alfahari da sanya harshen Hausa a manhajar shafin.
Mista Zuckerberg yana magana ne a rana ta farko ta ziyarar aikin da ya fara a birnin Legas na Najeriya, wacce ita ce ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka.Tuni ya gana da matasan da suke harkar kamfanonin fasahar zamani domin ya kara musu karfin gwiwa.

 

160830164427_e68e0d4c-1401-4ef6-9898-609730bcc0a2

Wata sanarwa da kamfanin Facebook ya fitar ta ce Mista Zuckerberg ya je Najeriya ne domin harkokin bincike na kasuwanci.”Mark zai yi saurari jama’a, ya dauki darasi da kuma hikomomi kan yadda Facebook zai taimaka wurin bunkasa harkokin sadarwa a Afirka,” in ji sanarwar.

Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa “zan dauki darasi kan yadda ake kafa kananan kamfanoni a fannin sadarwa a Najeriya.”Wannan wuri ya bani sha’awa sosai, kuma a shirye nake na koyi abubuwa masu da dama”.Ya kuma yi alfahari da amfani da harshen Hausa a manhajar ta Facebook, sannan ya ce za su ci gaba da sanya sauran harsunan Najeriya.

Kididdiga ta nuna cewa mutanen Najeriya sun fi na kowacce kasa masu ma’amala da kafar sada zumunta ta Facebook a nahiyar ta Afirka.

 

14095962_10103069173423651_6344352463424420323_n

Ya taso ne daga kasar Italiya, inda ya gana da PaparomaFrancis, sannan ya yi magana kan muhimmancin samarwa mutane damar yin hulda juna da yanar gizo musamman a wuraren da babu manhajar.

 

14195993_10103069392364891_3949740817451118641_o

You may also like