Shugaban Facebook Zuckerberg ya Birge ni sosai –  Buhari


Buhari ya bayyana hakan ne yayin da Zuckerberg ya kai ziyara Fadar shugaban kasan na Najeriya, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar dauke da sa hanun, mai baiwa shugaban shawara kan harkar ‘yan jarida Femi Adesina.
Fadar shugaban kasar ta ce, wannan ziyara ta Zuckerberg da irin kulawa da ya baiwa matasan kasar ta zo a kan gaba, domin hukumomin kasar na ta kokarin karawa matasa kwari gwiwar bunkasu dabarunsu na kasuwanci.“Ka burge ni da irin saukin kanka da kuma himmatuwa da ka yi wajen samarwa mutane ilimimusamman masu karamin karfi.” In ji Buhari.

Buhari ya kara da cewa, “a al’adunmu, ba kasafai ake ganin fitattun mutane kamar ka ba, ba mu saba ganin mutane kamar ka suna motsa jiki suna zufa a kan titi ba.”Yayin na sa jawabin,

 Zuckerberg, ya ce ya yi matukar jin dadin da yaga irin hazakar da matasake nunawa a duk wuraren da ya ziyarta a Najeriya.“Na ji dadi sosai da irin hazakar da na gani a wurin matasan da na tarar a wajen samar da fasaha na Yaba. Sun ainihin burge ni” In ji Zuckerberg.

Zuckerberg ya kai ziyara Najeriya ne tun a farkon makon nan, inda ya ziyarci wurare da dama ya kuma tattauna da matasa kan dabarun sarrafa manhajoji da na kasuwanci.

You may also like