Shugaban hukumar ICPC na farko, Mustapha Akanbi ya rasu


Shugaban Hukumar Hana Ci Da Karbar Rashawa ,wato ICPC, na farko, Mustapha Akanbi, ya rasu.

Akanbi ya mutu da farkon safiyar ranar Lahadi a wani asibiti mai zaman kansa dake Ilorin babban birnin jihar Kwara.

Ya rasu yana da shekaru 86 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Marigayin ya kasance tsohon shugaban kotun daukaka kara ta tarayya kuma yana rike da sauratar wakilin Ilorin.

Abdulrahman Ajidagba, wani makusancin marigayin kuma kwamishinan zaben jihar Nasarawa ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN rasuwar cikin wani gajeren sakon waya da ya aikewa kamfanin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like