Shugaban Hukumar Zaben Gambiya Ya Tsere


 

 

Rahotanni daga Gambiya na cewa shugaban hukumar zabe ta kasar ya tsere daga kasar sakamakon barazanar rasa ransa.

Iyalen Alieu Momar Njai, sun shaidawa masu aiko da rahotani cewa baya kasar kuma ba zasu fadi inda yake ba.

Saidai har kayo yanzu babu wata hukuma ko kafar gwamnati data tabbatar da hakan.

A farkon watan Disamban da ya gabata ne, shugaban hukumar Alieu Momar Njai ya ayyana Adama Barrow a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugabancin kasar bayan da ya doke shugaba mai ci Yahya Jammeh.

To sai dai shugaba Jammeh ya ki amince wa da shan kayi bayan ya zargi jami’an hukumar zaben da tafka kura-kurai, abin da ya tilasta masa garzayawa kotu don kalubalantar sakamakon.

You may also like