Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau Ya Umarci Limaman Masallatan Juma’a Da Suyi Addu’a Ta Musamman A Yau Juma’a 


Shugaban JIBWIS ta tarayyar Nijeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya umurci Limaman masallatan Juma’a dake fadin kasar nan, da su saka cikin hudubarsu na Juma’an gobe, in sha Allah, addu’ar zaman lafiya da fatan Allah Ya kara kare mu daga sharrin masu cutar da kuma kashe al’umma a masalatai, gidajenmu da wuraren gudanar da hidimomin  jama’a na rayuwa. 
Haka zalika Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari Allah Ya kare mana shi, ya kara masa lafiya da zama lafiya, Ya kara masa juriya, fasaha da kwazo cikin jagorancin da ya ke wa kasarmu Nigeria. 
Allah (SWT) Ya taimakemu baki daya, amin summa amin.

You may also like