Shugaban jami’iyar APC na jihar Kano ya sauka daga kan mukaminsa


Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyar APC na jihar Kano tsagin gwamna Abdullahi  Ganduje ya sauka daga mukamin shugabancin jam’iyyar.

Amma kuma an mika sunansa gaban majalisar dokokin jihar domin ta tantance shi a matsayin kwamishina a majalisar zartarwa ta jihar.

Ana sa ran Abbas zai bayyana gaban majalisar domin tantancewa.

Wannan sauyi da aka samu baya rasa nasaba da takun sakar da ake yi tsakanin tsohon shugaban da kuma mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafiz Abubakar.

Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da mataimakin gwamnan ya ce ba zai yi takara da gwamna da Ganduje ba a zaɓen shekarar 2019.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like