Da yammacin yau Litinin shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo gida Najeriya daga birnin London.
Shugaban kasar yaje London a duba lafiyarsa bayan da ya halarci babban taron majalisar dinkin duniya karo na 72 da ya gudana a birnin New York.
Dawowar shugaban kasar da yammacin yau ya jawo cinkoson ababen hawa sakamakon rufe titin zuwa filin jirgin saman Abuja da akayi na wucin gadi.
Shugaban kasar ya isa birnin New York a ranar 18 ga watan Satumba ya kuma baro birnin zuwa London a ranar Alhamis.
Wannan ne dai karo na uku da shugaban yake zuwa birnin London domin likitoci su duba lafiyarsa.