Ganawar Shuagaban Kasar Iran Da Ministan Harkokin Wajen Turkiya
Shugaban Kasar Iran Dr. Hassan Rauhani, ya ce; Yin aiki tare a tsakanin Iran da Turkiya shi ne ginshikin zaman lafiya a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya.
Shugaban na jamhuriyar musulunci ta Iran yana fadin haka ne a lokacin ganawa da ministan harkokin wajen kasar Turkiya Maulud Chus Aglu wanda ya ke ziyarar aiki anan Tehran.
Dr. Hassan Rauhani Rauhani ya kara da cewa; Kasashen Iran da Turkiya suna da matsaya guda akan muhimman batutuwa na yankin gabas ta tsakiya, sannan ya kara da cewa:
” Kare dukkanin iyakokin kasar Iraki da Syria, da kuma kafa gwamnatocin demokradiyya bisa yardar al’ummun kasashen.
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya yi ishara da juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Turkiya, sannan ya kara da cewa: Al’ummar Kasar ta Turkiya sun nuna rikonsu da tsarin demokradiyya.
A nashi gefen, ministan harkokin wajen kasar Turkiya Chavus Maulud,ya ce; Kare dukkanin iyakokin kasar Iraki da Syria za su amfani kasashen Iran da Turkiya.
A yau asabar ne dai ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya fara ziyarar aiki a nan Iran, domin tattauna batutuwan da su ke da alaka da gabas ta tsakiya.