Shugaban Maaikatan Jihar Abia Ya Mutu A London


Shugaban maaikatan jihar Abia Chief Chijioke Nwakodo ya mutu yanada Shekaru 56 a Asibitin dake Birnin Landan, kaninsa ya tabbatarwa manema labarai da mutuwarsa a umuahia.

An haifesa a shekarar 1961, yayi Shugaban Karamar hukumar Umuahia ta arewa daga 1999-2002, sannan yayi mai baiwa tsohon gwamnan Jihar Theodore Orji Shawara kan Harkokin tattalin Arziki.

Ya mutu yabar yara 2 sannan aka nadashi a matsayin Shugaban Maaikatan Jihar a 3 ga Watan Yuni 2015.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like