Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal Ya Amince Da Hukuncin Kotu
WASHINGTON, DC – A wata sanarwa da ya fidda a shafinsa na twitter, Lawan ya ce bayan tattaunawa da ‘yan siyasa abokan huldarsa da magoya bayansa ya yanke shawarar ba zai daukaka kara ba, ya amince da hukuncin kotun.

Bayan haka ya gode wa Sanata Ibrahim Gaidam na jam’iyyar APC da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, da kuma ‘yan mazabarsa saboda goyon bayan da suka bashi.

Lawan da Machina sun kwashe watanni suna sa-in-sa akan neman kujerar. A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Yobe ta umurci hukumar zabe ta INEC da ta amince da Machina a matsayin dan takarar kujerar dan majalisar dattawa.

Tun a shekarar 1999 aka fara zaben Lawal a majalisar wakilai, kafin daga baya aka zabe shi a majalisar dattawa, sannan a shekarar 2019 ya zama shugaban majalisar dattawan kasar.

You may also like