Shugaban Majalisar Dattawan Arewa Yayi Murabus Shugaban Majalisar Dattawan Arewa wadda, Farfesa Paul Unongo ya yi murabus daga mukaminsa bayan ‘ya’yan majalisar sun nesanta kansu daga kalaman da ya yi kan rikicin Fulani da manoma a Binuwai.

Farfesa Unongo dai, dan asalin Binuwai ne kuma ya fito fili ne ya zargi wasu ‘yan Arewa da daurewa Fulani gindin suna kisan gilla wanda hakan ya janyo Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ya maka shi kotu inda ya nemi ya biya shi diyyar Naira Bilyan 200 bisa alakanta shi da daukar nauyin kungiyar Fulani ta Miyetti Allah.

You may also like