Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa Ya Musalta Zargin Da Ake Masa Na Dukan Ɗansanda


adamawa

Kakakin majalisar dokoki ta jihar Adamawa, Alhaji Kabir Mijinyawa ya musalta rahotannin dake cewa ya doki wani jami’in ɗan sanda dake aiki tare dashi , bayan da ɗan sandan yayi ƙorafin rashin biyanshi kuɗaɗen alawus.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, wacce mai magana da yawun majalisar dokokin ya sanyawa hannu Yahaya Deji, ya bayyana labarin a matsayin “marar tushe, ƙarya ,da babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan a ciki”

Mijinyawa yace a matsayinsa na ɗan majalisa yana girmama doka, saboda haka bazai iya aikata irin wannan mummunan aiki ba akan wani.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, ya rawaito cewa mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Adamawa, Othman Abubakar yace ƴan sanda suna binciken abinda yafaru.

Abubakar yace akwai zargin da ake cewa shugabana majalisar dokokin Jihar Adamawa ya daki wani ɗan sanda dake aiki tare dashi.

You may also like