Lr: Daga Engr Magaji Abdullahi Mallammadori
Shugaban majalissar dokokin jihar Jigawa, Honarabul Idris Garba Kareka, ya hau babur din dan acaba, domin gaisawa da al’ummar mahaifarsa ta karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa.
Duk da yana da motoci na alfarma wanda doka ta tanadar masa, a cewar wani tsohon dan siyasa a jihar Jigawa, ya yi haka ne domin kara kusantar talakawa, gami da nuna musu rashin kyama.
Mutane da dama sun yi farin ciki da yin hakan, duba da yadda wasu masu mulki a Nijeriya suke gudun al’ummarsu, inda za ka dinga ganin su a jibga-jigan motoci na alfamar gami da rufe gilashi motocinsu da bakin gilashi wato tintad, duk dan su batar da sawun al’umma.