Mista Peter Maurer shugaban masu samar da agaji gaggawa (ICRC) ya kai ziyara jihar Borno inda ya jajantawa wadanda aka jefawa bom bisa kuskure a garin Rann.
Shugaban ya nuna damuwarsa bisa kuskuren da mayakan saman Nijeriya suka yi. Wanda ya kai ga hallaka mutanen da suka yi gudun hijira da ma’aikatan jinya.