
Asalin hoton, Alhassan Doguwa Facebook
Bayan zaɓen cike-giɓi, INEC ta bayyana Alhassan Ado Doguwa a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaɓen ɗan majalisar wakilai daga mazaɓar Doguwa da Tudun Wada.
Karo na biyar kenan, da ɗan majalisar na tarayya ke samun nasarar zuwa majalisar wakilai daga Kano tun bayan dawowar Najeriya mulkin dimokraɗiyya a 1999.
An soke nasarar da ya samu tun farko, bayan zaɓen 25 ga watan Fabrairu, saboda jami’in sanar da sakamako, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya ce “tursasa masa” aka yi.
Ya dai ce sai an sake kaɗa ƙuri’a a tasoshin zaɓe 13.
Sai dai, jami’in sanar da sakamako a zaɓen cike-giɓi na mazaɓar, Farfesa Sani Ibrahim a ranar 15 ga watan Afrilu, ya ayyana Alhassan Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara bayan wannan zaɓe.
Alhassan Ado Doguwa, wanda shi ne shugaban masu rinajye a majalisar wakilai ya yi nasara ne bayan ya samu ƙuri’a 41,573, inda babban abokin fafatawarsa, Yusha’u Salisu na NNPP ya samu ƙuri’a 34,831.
Zaɓen dai, yana ɗaya daga cikin masu cike da taƙaddama a 2023, saboda tashin hankalin da aka samu a wancan karo, rikicin da ya yi sanadin ƙone-ƙone da halakar mutane.
Yana ɗaya daga cikin zaɓukan ‘yan majalisar wakilai da na jihohi har guda 16 da aka ƙarasa ranar Asabar a cikin jihar Kano.
Bayan zaɓen ɗan majalisar wakilai na mazaɓar tarayya ta Doguwa da Tudun Wada, an yi makamancin wannan zaɓe a mazaɓar Fagge.
Kuma jami’in sanar da sakamako, Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya bayyana cewa Muhammad Bello Shehu na jam’iyyar NNPP ya lashe zaɓe inda ya kayar da abokan fafatawarsa ciki har da Suleiman Aminu Goro, ɗan majalisar da ya wakilci mazaɓar tarayya ta Fagge har karo uku.
Muhammad Bello Shehu dai samu nasara ne da yawan ƙuri’a 19,024.
Ƙarin wuraren da aka yi zaɓen cike-giɓin a cewar wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na intanet a Kano, sun haɗar da ƙananan hukumomi 14, inda aka ƙarasa zaɓukan ‘yan majalisar dokokin jiha.
Ga ƙananan hukumomin da aka yi zaɓen
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Takai
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Warawa
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Wudil
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ungogo
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gwarzo
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Tudun wada
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gezawa
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Makoɗa
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gabasawa
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Garko
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Gaya
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Dawakin Tofa
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Danbatta
Mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha ta Ajingi