Shugaban PDP da sauran Magoya bayansa a Gwaga sun sauya sheka zuwa APC


Shugaban jam’iyar APC a mazabar Gwaga a Abuja dake karamar Hukumar AMAC a Abuja, Murtala Muhammad Haruna ya sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC.

Ya ce ya bar jam’iyar APC ne saboda kyawawan sauye-sauye da suke faruwa tun lokacin da  Shugaban AMAC, Alhaji Abudullahi Adamu Candido ya karbi ragamar tafiyar da shugabancin karamar hukumar.

Haruna wanda shugaban karamar hukumar ya karbe shi tare da wasu magoya bayansa 500 ya ce zai taimaka dari bisa dari domin tabbatar da cewa sauyin da aka samu ya cigaba ba, ba baya ba.

“Sama da mutane 500 da suka fito daga bangarori na rayuwa daban-daban suke sauya sheka tare da ni a Gwaga.Na kasance a jam’iyar PDP tun shekarar 1998 An nada ni shugaban jam’iya a shekarar 2016 har ya zuwa jiya. Yau na zo APC domin na taimakawa yan uwana  dmmu tabbatar mun ciyar da Gwaga, AMAC, Abuja, da kuma Najeriya baki daya gaba.”

Da yake jawabin maraba da tsohon shugaban mazabar Candiodo  yace APC tana maraba da mutane inda ya  shawarci sauran jama’a da  su shigo cikin jam’iyar

You may also like