Shugaban PDP na kasa, Yarima Uche Secondus ya kai ziyara jihar Binuwai don jajantawa gwamnatin jihar da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kai shi.
Tun da farko, jam’iyyar PDP ta kalubalanci Shugaba Buhari kan yadda ya ki Ziyartar jihar Binuwai don ya jajanta masu kan rashin da aka yi inda jam’iyyar ta nuna cewa irin wannan hali na Shugaban ya nuna cewa yana bayar da mafaka ne ga fulani ‘yan uwansa.