Shugaban PDP Ya Maka Lai Muhammad A Kotu


Shugaban jam’iyyar PDP na Kasa, Uche Secondus ya maka Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed kotu bisa bayyana sunansa cikin jerin barayin gwamnati inda ya nemi diyyar Naira Bilyan 1.5 bisa abin da ya kira bata masa suna.

A cikin karar da ya shigar a Babban kotun jihar Rivers, Shugaban jam’iyyar ya nemi kotun ta tilasta Ministan Yada Labaran kan ya janye wannan ikirarin tare kuma da neman gafararsa a rubuce.sannan kuma yana bukatar kotu ta dakatar da Ministan daga ci gaba da saka sunansa cikin jerin barayin gwamnati a nan gaba.

You may also like