Shugabanni Sun Jaddada Muhimmancin Zaman Lafiya A Wajen Bikin Cikar Janar Babangida Shekara 80
Janar Abdussalam Abubakar, wanda shi ma tsohon shugaban Najeriya ne ya bayana cewa idan babu zaman lafiya babu kasa.

A tsokacin da ya yi payin bikin, Janar Abubakar ya yi kira ga dukkan jama’a, mata da maza, yaro da babba da a hada da su ba da gudunmowarsu don samar da zaman lafiya.

Shi ma tsohon gwamnan jihar Neja Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ya ce hakkin shugabanni ne su kare rayukkan jama’a da dukiyoyinsu, ya kara da cewa ko a tsarin kunin mulki shi ne na farko.

Su ma dai wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana cewa akwai bukatar ‘yan Najeriya su maida hankali wajen hada kai domin dorewar kasar a matsayin kasa guda.

An dai hana manema labarai shiga gidan tsohon shugaban kasa Babangida a lokacin bikin al’amarin da ya hana samun damar zantawa da shi.

Amma a wata zantawa da muka yi da shi a kwanakin baya game da nuna bukatar yin adalci ga shugabannin siyasa. tsohon shugaban ya ce dole ne shugabanni su zama masu gaskiya, masu adalci su kuma san kan siyasa da taimakawa magoya bayansu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

You may also like