Shugabannin APC Na Yankin Yarabawa Sunyi Taron Hadin KaiShugabannin APC na yankin Yarbawa sun gudanar da wani taro na neman hadin kan jigogin siyasar yankin don samun cimma nasarar samar wa yankin abubuwan da take bukata daga gwamnatin tarayya.
Taron dai ya samu halartar tsohon Gwamnan  jihar Legas, Bola Tinubu, Ministan Wutar Lantarki, Babatunde Fashola, tsohon Gwamnan Oyo, Olusegiun Osaba, Gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun da takwarorinsa na jihohin Osun, Rauf Aregbesola da na Legas, Akinwuni Ambode.
Sauran sun hada da Ministan Labarai, Lai Mohammed, Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu sai Chief Bisi Akande; tChief Segun Oni; tsohon Gwamnan Osun, Olagunsoye Oyinlola; Shugaban. Masu Ladaftarwa na Majalisar Dattawa, Sola Adeyeye; Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai,  Femi Gbajabiamila.

You may also like