Shugabannin Arewa ta Tsakiya sun amince da takarar Buhari a karo na biyuGwamnoni da kuma wasu manyan yan siyasa da suka fito daga yankin arewa ta tsakiya sun nemi shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake tsayawa takara a karo na biyu a shekarar 2019.

Shugabannin  sun cimma wannan matsaya ne a wani taro shiyar Arewa ta Tsakiya da akayi na kungiyar magoya bayan shugaba Buhari wanda ya gudana ranar Talata a Abuja.

Wadanda suka nemi Buhari ya yi takara a a karo na biyu sun hada da gwamnan jihar Plateau Simon Lalong, Samuel Ortom na jihar Benue,gwamna Tanko Al-Makura da ya samu wakilcin mataimakinsa, Silas Agara, da kuma tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata George Akume da sauransu.

Wannan cigaba da aka samu na zuwa ne bayan da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC suka nemi a amince da Buhari a matsayin dan takara yayin taron  kwamitin zartarwar uwar jam’iyar da aka yi a Abuja.

George Akume ne ya sanar da kudirin neman Buhari ya tsaya takara a karo na biyu inda ya samu goyon bayan gwamna Lalong.

Yayin da sauran mutane dake wurin da suka hada da jiga-jigan jami’iyar da suka fito daga shiyar suka amince.

Sai dai rashin gani fuskokin wasu mutane a taron kamar shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na iya jefa shakku kan ikirarin da shugabannin suka yi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like