Shugabannin ECOWAS Ba Su Amince Da Ba Wa Jammeh Kariya Ba


 

 

Ministan harkokin wajen kasar Senegal Mankeur Ndiaye ya bayyana cewar shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen Yamamcin Afirka (ECOWAS) ba su amince da batun ba wa tsohon shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh kariya ba.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar ministan harkokin wajen Senegal din  Mankeur Ndiaye ne ya shaida masa haka inda ya ce a yayin tattaunawar da aka yi don cimma matsayar sauka daga karagar mulkin Yahya Jammeh, shugabannin kungiyar ECOWAS din ba su amince da batun da aka kawo na ba shi kariya ba.

Ministan harkokin wajen na Senegal yana fadin hakan ne a matsayin mayar da martani ga wata sanarwa da ke cewa kungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun amince su ba Mr. Jammeh kariya, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma ta saukarsa daga mulki.

Ana zargin tsohon shugaban Gambiyan dai da take hakkokin bil adama tsawon shekaru 22 na mulkinsa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like