Shugabannin Jam’iyyar APC Ba Za Su Iya Sake Tsayawa Takara Ba – Buhari


Shugaba Muhammad Buhari ya jaddada cewa shugabannin APC na yanzu ba za su iya sake shiga takarar neman kujerarsu bisa dokar jam’iyyar wadda ta tanadi cewa duk wanda ke son tsayawa takarar dole ya sauka daga kujerarsa a tsakanin kwanaki 30 kafin zabe.

Sai dai kuma Shugaban ya nuna cewa idan shugabannin jam’iyyar na bukatar tsayawa takarar, sai sun samu Izinin yin hakan daga kwamitin gudanarwar jam’iyyar wanda kuma ya ce dole su gaggauta yin haka idan har sun yanke shawarar shiga zaben.

You may also like