Shugabannin Jam’iyyu Da Kwararru Sun Yi Takaicin Matsayin Kotun Kolin Najeriya Kan Wa’adin Canjin KudiABUJA, NIGERIA – Kotun Kolin dai ta dage sauraron karar da wasu Jihohi biyar suka shigar zuwa ranar 22 ga wannan wata, kan kalubalantar wa’adin da Babban Bankin Najeriya CBN ya gindaya kan tsofaffin takardun kudi na 200, 500 da kuma 1000.

Jihohin Kaduna, Kogi, Zamfara, Neja da Ogun su ne suka shigar da Gwamnatin Tarayya kara kan wa’adin da CBN ya sa a kan sauya tsofaffin kudi zuwa sabbi.

Sabbin kudin Naira

Sabbin kudin Naira

Babban Bankin ya mayar da wa’adin da ya gindaya a baya na kare abin da ya kira martabar takardar kudin kasar daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu, to saidai wannan mataki ya ja ce-ce-ku-ce a daidai lokacin da yan Najeriya ke fuskantar mawuyacin hali wajen samun sabbin kudin bayan ana kin karbar tsofaffin a ko ina a cikin kasar.

Shugaban Jamiyyar SDP Shehu Gaban ya yi tsokaci akan batun da cewa ba abin alfahari ba ne a ce kasa da ke shirin zabe ta shiga wannan hali na kakanakayi a kan kudi, a daidai wannan lokaci. Gabam ya ce Gwamnati dole ta dauki matakin kawo dauki cikin hanzari saboda mutane su samu kudaden su, sannan hankali ya kwanta.

Babban bankin Najeriya CBN

Babban bankin Najeriya CBN

Shi ma Shugaban Jamiyyar Accord Mohammed Lawal Nalado, ya hada da rokon a hanzarta daukar matakin gaggawa na sauwaka wa jama’ar kasar domin an shiga halin kunci. Nalado ya ce Jam’iyya tana goyon bayan wannan tsarin, amma ta na sukar wannan lokaci da aka shirya aiwatar da tsarin. Nalado ya ce babu wanda aka bari a baya a wahalar da tsarin ya kawo ganin cewa abinci ma yana nema ya gagari talakan kasar.

Amma ga daya cikin masu mu’amala da kudin chanji Umar Garkuwa ya nuna bakin cikin abinda ke faruwa da tsarin CBN.

Garkuwa ya ce talaka ya kashe kudinsa wajen tallafa wa Shugaba Buhari a lokacin da yake nemar kuri’u a shekarun baya, amma a yau talaka ne yake shan wahala. Garkuwa ya ce ya yi imanin cewa a duk inda talaka ya samu kanshi a cikin irin wannan hali, a koma ga addu’a. Allah zai kawo mafita.

Kotun koli ta ce duk da daga sauraron karar da Jihohi suka shigar zuwa ranar 22 ga wannan wata, umurnin da ta bayar a ranar 8 ga watan Fabrairu cewa a ci gaba da amfani da tsofaffin kudin tare da sabbin, yana nan daram.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like