Shugabannin Kananan Hukumomi Bakwai Sun Goyi Bayan Dakatar Da Sanata Shehu Sani Daga APC


 

Shugabannin Kananan hukumomi guda bakwai dake karkashin mazabar Sanata Mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani sun nuna goyon bayansu ga dakatar da shi da jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta yi.

Shugabannin kananan hukumomin sun hada da:

  1. Magaji Bala, Shugaban jam’iyyar APC daga Karamar hukumar Chukun.
  2.  Abdullahi Jariri, Shugaban jam’iyyar APC daga Karamar hukumar Birnin Gwari.
  1. Musa Shehu, , Shugaban jam’iyyar APC daga Karamar hukumar Kaduna North.
  2. Ibrahim Musa, Shugaban jam’iyyar APC daga Karamar hukumar Giwa.
  3. Halidu Bature, Shugaban jam’iyyar APC daga Karamar hukumar Igabi.
  4. Bala Wahab, Shugaban jam’iyyar APC daga Karamar hukumar Kajuru.
  5. Alhaji Ibrahim Y. Soso, Mai rikon kwarya, Shugaban jam’iyyar APC daga Kaduna South.

Sai dai Sanata Shehu Sani ya ce bai amince da dakatarwar ba kuma wannan takardar ba ta da wani tasiri a wajensa da magoya bayansa, inji shi.

You may also like