Shugabar Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Duniya Na Kan Hanyarsa Ta Zuwa Iran.


 

 

 

Yokiya Amano Zai Zo Iran A Gobe Lahadi

Shugaba Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Kasa da Kasa, Yokiya Amano zai kawo ziyarar aiki nan Iran a gobe lahadi.

Majiyar hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ta ce ziyarar ta Amano manufarta tattaunawa da jami’an Iran akan yarjejeniyar Nukiliya.

Amano Zai yi ziyarar ta shi ne adaidai lokacin da Amurka ya ke karya yarjejeniyar ta Nukiliya ta hanyar kakabawa Iran takunkumi.

Hukumar makamshin Nukiliyar ta duniya ta sha sanar da cewa; Iran din tana aiki da yarjejeniyar.

You may also like