Darakta Janar ta Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF Christine Lagarde ta yi gargadi game da yadda hasashen cigaban tattalin arziki na duniya na shekaru 5 ya ke dada ja da baya.
Lagarde ta tattauna da kamfanin dillancin labarai na Rueters kafin a fara taron G20 ranar Litinin a kasar China.
Ta ce, tun shekarar 1990 tattalin arzikin duniya bai taba karyewa kamar a wannan lokaci ba.
Ta kara da cewa, harkokin siyasa a duniya su suke dakile cigaban tattalin arziki kuma akwai bukatar a bayar da damar zuba jari da kasuwanci ba tare da hantara ba.
Lagarde ta kuma kara da cea, fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai ya sake karya tattalin arzikin duniya.