Shugabar Tanzania ta dage hanin yakin neman zabe



Samia Suluhu Hassan is Tanzania's first female president

Asalin hoton, Getty Images


Shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta janye wata dokar hana gudanar da gangamin yakin neman zane da tsohon shugaban kasar mai ra’ayin rikau John Magafuli ya kafa shekaru shida da suka gabata.



Ta ce wannan shawarar da ta yanke na karskashin wani shirin hada kai da sake gina kasar ne mai suna 4R.



Ta lura cewa jam’iyyun siyasa a kasar na da ‘yancin gudanar da yakin neman zabensu sai dai ta bukace su da su guji zagin juna kana su kasance masu mutunta juna.


Toshon shugaba Magafuli ne ya kafa dokar hana jam’iyyun gudanar da gangamin yakin neman zabe, matakin da wasu ke kallo a matsayin rage karfin da jam’iyyun ke da shi.



Ta sanar da matakin ne yayin wani taro da ta kira tare da manyan jami’an da ke jagorantar jam’iyyun siyasa.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like