SHURE-SHURE BOKO HARAM KE YI. 


Hedkwatar Tsaro ta Najeriya ta ce bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar wanda ya nuna sallar Idi a Dajin Sambisa shure-shure ne “wanda Hausawa suka ce ba ya hana mutuwa”.
Mai magana da yawun hedkwatar, Birgediya Janar Rabe Abubakar ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da ‘yan jaridu.

“Suna so ne su gwada wa mutane cewa har yanzu suna nan…amma su kansu sun san matsayinsu”, inji Janar Abubakar.

Da yake magana a kan yawan mutanen da suka halarci sallar Idin, kuma suke tare da ‘yan kungiyar ta Boko Haram, kakakin na hedkwatar tsaron Najeriya ya ce, “Wadanne mutane ne? Ba wani abu ba ne da zai ba da mamaki.

“Illa iyaka mun san cewa maganar Boko Haram a Najeriya ko sun so ko sun ki, wurin kawai da suke da shi ke nan–kafafen sadarwa na zamani”.

Ranar Talata ne dai kungiyar ta Boko Haram ta wallafa wani faifan bidiyo a shafin Youtube tana cewa tana nan da karfinta sabanin ikirarin da gwamnatin Najeriya ke yi cewa ta kawo karshen mayakanta.

Hoton bidiyon ya nuna sallar Idi a masallatai uku, ciki har da rufaffen masallaci wanda aka cika makil, jagoran sallar kuma ya aike da sako ga hukumomin Najeriya cewa “kada fa su ce {wannan} tsohon sako ne wanda ya wuce a baya: yau ne muka yi shi, ranar Litinin, 12 ga watan September, shekara ta 2016


Like it? Share with your friends!

0

You may also like