Shu’umar Dabba Mai Cinye Mutane ta Sake Bayyana A Kano


Bayan kashe dabbar nan da ake zaton aljani ne da mafarauta sukayi a garin Beli dake nan Kano, yanzu haka wasu irin ta guda biyu sun sake bayyana.

A daren shekaranjiya nedai aka debo wasu mafarauta suka shigo garin sukai ta yin hayaki da talatainin dare, harma suka sami nasarar hallaka dabbar mai kama da kare, yayin da ta wasu bangarorin take kama da kura, bayan shafe tsawon daren suna artabu.

Kwatsam kuma yanzu haka kamar yadda rahotanni suka ishe ni yanzu haka daga garin na cewa wasu biyu irin ta sun sake bayyana.

Wacce aka hallaka dai ita kadai ma takan lamushe rago 12 da karnuka 2, sai dai akwai washe gari a tashi aga kai da kafa da fata, ko digon jinni ba’a gani.

You may also like