Siyasa: An Samu Baraka A Tafiyar Kwankwasiyya An samu baraka a tafiyar masu akidar Kwankwasiyya bayan da Shugaban Riko na kasa a tafiyar, Nuruddeen Muhammad Inuwa ya kalubalanci matakin korar sa da aka yi sakamakon laifin cin amanar tafiyar da wani kwamitin ya same shi laifin aikatawa.

Shugaban Rikon wanda kuma yana daya daga cikin masu taimakawa Gwamnan Filato, ya ce madugun tafiyar na kasa ne ya dauki nauyin wannan yunkuri na korar sa saboda wani rashin jituwa da ke tsakaninsu.

You may also like