Siyasa: Sanata Isa Misau Ya Caccaki Buhari 



Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Sanata Isa Misau ya caccaki Shugaba Muhammad Buhari kan cewa mafi yawan mutanen da ya nada a cikin gwamnatinsa, ba su da kwarewa.
Sanatan ya ce kashi 50 na ministocin da Buhari ya nada duk ba su aikin komai inda ya nuna cewa Shugaban ya bar wasu tsiraru suna yanke shawarwari game da wadanda za su rike mukaman gwamnati.
Misau ya bayar da misali da nadin da Buhari ya yiwa Ahmed Abubakar a matsayin Shugaban hukumar leken Asiri ta kasa kasancewa shi mutum ne wanda kowa ya san ya kasa cin jarrabawar karin girma a lokacin yana aiki a hukumar.

You may also like