Siyasar Kano: Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Gayyaci Kwankwaso Don Jin Ba’asin Yadda Wasu Makudan Kudade Suka Yi Batar Dabo A Zamaninsa


kwankwaso

Kamar yada aka ji a baya mai girma gwamna jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje na nuna cewa ba zai binciki gwamnatin da ya gada ba wadda ya ce ta yi aiki kuma ta tabka aika-aika tsawon shekaru hudu.
Amma a gefe guda kuma jami’an gwamnatin Gandujen masu jibi da binciken kudi a jihar na nuna cewa suna aiki tukuru don gabatar da aika-aikar da suka binciko gwamnatin da suka gada tayi ga majalisar dokoki ta jihar kano.

Babban mai binciken kudi na jihar Kano ya shaidawa manema labarai a jiya Litinin cewa
kadan daga aika-aikar da suke zargin Gwamnatin kwankwaso ta yi na nuni da cewar ta dibi kudi daga asusun hadaka na jihar da kananun hukumomi har Naira Bilyan Dari biyu da sha uku (213bn) kuma kudin sun bata bat a aljihun sanata Kwankwaso, Inji Mai binciken kudi na jihar kano.

Babban mai binciken kudin yace kwankaso ya kuma yiwa kansa gwanjon motoci masu numfashi guda 12 kan miliyan uku rak, ciki har da mota mai sulke.

Wata badakalar kuma itace wadda mai binciken kudin ya ce
gwamnatin kwankwaso ta kashe biliyan dari da ashirin (120bn) ba bisa ka’ida ba a shekarar 2013 kawai!

Haka zalika Auditor-Janar din yace kudade masu nauyin Biliyan Dari biyu daTalatin (230bn) suma an neme su sama da kasa an rasa bayan da Gwamnatin tarayya ta Jonathan Goodluck ta aiko domin tallafawa rayuwar Matasa da sunan Sure-P.

Ana dai sa ran majalisar jihar kano za ta saka rana domin gayyato Sanata kwankwaso gabanta domin yi mata bayanin inda wadannan kudade suka zurare kuma suka bata bat.

You may also like