‘Siyasar Obi da Jam’iyyar LP ta mutu murus, saura jana’izarta’



Peter Obi
Bayanan hoto,

Peter Obi ne ya zamo na uku cikin jam’iyyun da suka samu mafi yawan kuri’u a zaben shugaban kasa na shekarar 2023

A Najeriya, cacar-baki ta kaure tsakanin `yan jam`iyyar APC mai mulkin kasar da na jam`iyyar Labour tun da aka ji wata tattaunawar waya tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam`iyyar Labour, Peter Obi da Bishop David Oyedepo na majami`ar Living Faith Church.

A karshen mako ne jaridar People Gazzete ta wallafa wannan murya da aka kwarmata, tsakanin Peter Obi da babban Bishop David Oyedepo.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta a kasar, musamman ma yadda aka ji dan takarar yana rokon malamin addinin kiristan ya taimaka wajen nema masa goyon bayan mabiya addinin kirista da ke shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da kuma shiyyar arewa ta tsakiyar kasar

Ya dai alakanta siyasar da takararsa tamkar fafutuka da suke yi yaki ne na addini, har ma ya tattabar masa cewa ba za su yi da-na-sanin goya masa baya ba.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like