Sojan Da Ya Nemi Yin Soyayya Da Matar Aure A Jihar Kogi Ya Shiga hannun Mafusata Wasu fusatattun matasa sun kaiwa wani soja farmaki bisa zarginsa da neman soyayyar wata matar aure a unguwar Gadumo dake Lokoja, Jihar Kogi.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne daf da wani gidan man fetur dake unguwar ta Gadumo ranar Talata da yamma.

Wani shaidar gani da ido dake kasuwanci kusa da wurin da abin ya faru ya ce sojan, da bai dade da zuwa garin ba daga Legas, yana ta kaiwa matar auren farmaki amma tana zukewa tare da bayyana masa cewar tana da aure.

Shaidar ya kara da cewa sojan bai daina kula matar ba duk da ta fada masa ita matar aure ce. Hakan ya saka mijin matar ya tunkari sojan har suka yi cacar baki.

Majiyar jaridar Daily Trust ta shaida mata cewar wasu fusatattun matasa a unguwar sun shigarwa mijin matar domin taya shi fada da sojan.

Shaidar ya ce sojan ya sha duka a hannun matasan kafin daga bisani wasu abokan aikin sojan su zo su kwace shi.

Da aka tuntubi kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Kogi, Mista Williams Aya, ya ce ba sanar da hukumar ‘yan sanda faruwar lamarin ba.

Saidai ya ce jami’insu mai kula da ofishin unguwar da abin ya faru (DPO) ya tabbatarwa hukumar cewa ya fahimci an samu hargitsi a unguwar amma koda ya isa wurin sai aka fada masa cewar sojoji sun tafi da sojan. Kazalika ya ce jama’a sun ki bawa DPO din bayanin abinda ya faru.

You may also like