Dakarun kasar Nijar da na Chadi sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram akalla 38 yayin wata karawa da suka yi a kauyuka biyu dake kan iyakan kasashen biyu.
Majiyoyin soji na cewa soja biyu na kasashen suka mutu yayin gumurzu da aka yi yankin garin Toumour.
Bayanai na cewa Sojan hadin guiwa tare da na Nigeria sunyi katari wajen kama makamai masu tarin yawa daga mabuyar ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
Ya zuwa yanzu ‘yan kungiyar Boko Haran a wannan yanki sun kashe dubban mutane da tilastawa mutane sama da miliyan biyu da dubu dari hudu barin muhallin su.